Labaran chikin kasa Nigeria :: Na sanar da shugaba Buhari cewa ba na son dawowa majalisarsa - Minista - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: Na sanar da shugaba Buhari cewa ba na son dawowa majalisarsa - Minista

<
Karamin ministan harkar noma da ci gaban karkara, Sanata Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa ya fada ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ba zai so dawowa a matsayin minister a majalisar sa ba.
Lokpibiri yace maimakon haka ya fada ma Shugaban kasar cewa zai tsaya takarar gwamnan jihar Bayelsa.
Ministan ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Channels TV, inda ya kara da cewa ya koyi abubuwa da yawa a karkashin shugaba Buhari sannan kumaa cewa yana Allah-Allah ya zama gwamnan Bayelsa domin ya baje kolin dukkanin abubuwan da ya koya.
Na sanar da shugaba Buhari cewa ba na son dawowa majalisarsa - Minista
"Na koyi abubuwa da dama a shekaru hudu da nayi fiye da abunda na koya a shekaru 12 da nayi a majalisa. Ina so na kai darusan da na koya gida sannan naga yadda za mu iya gina Bayelsa fiye da mai."
KU KARANTA KUMA: Dankari: An kama wata mata dake kai wa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano
Yace: “Na gana da Shugaban kasa yan kwanaki da suka gabata sannan na fada masa cewa ina sson takarar gwamna a Bayelsa bayan nag ode masa kan nada ni da yayi a matsayin minista.
“Sylva ba ubangida na bane. Lokacin da na kasance kakakin majalisa a 1999 shi yana a matsayin mai ba da shawara na musamman ga Alamieyeseigha. Lokacin da na je majalisar dattawa, sai ya zama gwamna."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.