Labaran chikin kasa Nigeria :: Maine dalil da yasa Ana yi wa dokar da ta kafa EFCC kwaskwarima a Majalisar Tarayya? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: Maine dalil da yasa Ana yi wa dokar da ta kafa EFCC kwaskwarima a Majalisar Tarayya?

< ‘Yan majalisar tarayya a Najeriya za su yi wani yunkurin karshe da zai iya fatattakar shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu daga ofis ta hanyar yi wa dokar da ta kafa hukumar a 2004 wasu kwaswarima.
Tuni dai wannan kudiri ya samu shiga a majalisar wakilai inda ake kuma sa rai Sanatoci su kammala na su aikin a cikin makon nan. Sabon kudirin da aka kawo yayi wa dokar nada shugaban EFCC garambawul.
Idan wannan kudiri ya samu karbuwa, zai zama cewa dole sai jami’in ‘dan sandan da ya kai akalla Mataimakin sufeta na ‘yan sanda na AIG, ne zai iya rike hukumar EFCC a maimakon matimakin kwamishina.
Majalisar za ta so a sauke Ibrahim Magu wanda CP ne daga shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, a maye gurbinsa da wani babban jami’in da ya kai akalla matakin AIG.
KU KARANTA : Ahmad Lawan yayi magana a kan albashin Sanatoci
Magu wanda yake ta fama da tirka-tirkar ‘yan majalisa yana kan mukamin Kwamishinan ‘yan sanda ne bayan ya samu karin girma kwanaki. Sau 2 ana kokarin a tabbatar da shi amma majalisar dattawa ta ki.
Majiyar mu ta bayyaana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai amince da wannan kudiri idan aka kawo sa gabansa ba. A makon gobe ne dai ‘yan majalisar za su yi zaman karshe domin a kafa sabon gwamnati.
Haka zalika ‘yan majalisar su na so shugaban EFCC ya zama yayi shekara 15 zuwa 20 yana aiki, ko ya zama yana da ilmin shari’a. Bayan nan kuma an canza sharudodin rike Sakatare a hukumar ta EFCC na kasa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.