Lafiya jari :::: Lafiya uwar jiki: Amfanin Bagaruwa 10 a jikin dan Adam - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Lafiya jari :::: Lafiya uwar jiki: Amfanin Bagaruwa 10 a jikin dan Adam

<
Binciken masana ya tabbatar da cewar itacen bagaruwa na da matukar amfani sosai tun jikin dan Adam kama daga ganye, itace da kuma ‘ya’yanta.
Noman itacen Bagaruwa ya fi yawa a busassun wuraren sannan kasar Australia da kasashen Larabawa na cikin kasashen da suka fi nomanta.
Lafiya uwar jiki: Amfanin Bagaruwa 10 a jikin dan Adam
Ga amfanin da yake yi a jikin mutum.
1. Bagaruwa na maganin tsutsar ciki.
2. Itacen bagaruwa na maganin gudawa mai tsanani.
3. Yana kuma kawar da matsalar zubar jini.
4. Bagaruwa na maganin ciwon hakori: Ana daka 'ya'yan Bagaruwa a riga zubawa ko kuma a samu 'ya 'yan ta wayanda basu bushe ba a riqa matsa ruwanta a cikin wurin.
5. Bagaruwa na maganin ciwon sikari wato ‘Diabetes’.
6. Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki.
7. Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata.
8. A samu ganyen Bagaruwa a tafasa idan ya tafasu a juye a buta a riga wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido
KU KARANTA KUMA: Zargin zamba: Kotu ta ki ci gaba da shari’an Babachir Lawal
9. Yana kara karfin mazakuta.
10. Bagaruwa na maganin cutar Hepatitis C.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.