Labaran wassani :::: Chelsea ta koma ta uku a teburin Premier - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran wassani :::: Chelsea ta koma ta uku a teburin Premier

<
Chelsea ta koma mataki na uku a teburin Premier, bayan da ta doke West Ham United da ci 2-0 a wasan mako na 33 da suka kara a Stamford Bridge.
Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Eden Hazard a minti na 24 da fara tamaula, sannan ya kara na biyu daf da za a tashi daga fafatawar.
A karawar farko da West Ham United ta karbi bakuncin Chelsea ranar 23 ga watan Satumbar 2018, sun tashi karawar 0-0.
A ranar 3 ga watan Afirilu, Chelsea ta doke Brighton da ci 3-0 a kwantan gasar Premier da suka yi a Stamford Bridge.
Kawo yanzu Chelsea ta koma ta uku a teburin Premier da maki 66, sai Tottenham ta hudu da maki 63, ita ma Arsenal maki 63 ne da ita, amma ta yi kasa zuwa matsayi na biyar.
Chelsea za ta ziyarci Slavia Prague a wasan farko na daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa da za su kara ranar 11 ga watan Afirilu.
Kungiyar ta Stamford Bridge wadda ke fatan kammala Premier bana cikin 'yan hudun farko za ta ziyarci Liverpool ranar 14 ga watan na Afirilu, tana kuma da karawa da Manchester United nan gaba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.