Labaran chikin kasa Nigeria ::: Mutane 13 Sun Mutu a Bauchi a Hatsarin Moto - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Mutane 13 Sun Mutu a Bauchi a Hatsarin Moto

<
A wani al'amari mai bakanta rai, mutanen jahar Bauchi sun yi rashin wasu bayin Allah wajen 13 a wani hadarin mota, baya ga wasu kuma da su ka ji raunuka.
Masarautar Bauchi da ma illahirin al’ummar jahar Bauchi na cikin kaduwa da alhinin bayan wani mummunan rashi na wasu bayin Allah a wani hadarin mota da ya faru da yammacin jiya Lahadi.
Cikin mutane 13 da su ka rasa rayukansu har da wani mai suna Jamalu Ahmed Yari, dan gidan sarautar yarin Bauchi, da matarsa da kuma ‘ya’ayansa guda biyu masu shekaru uku da kuma shekara biyar, da kuma kanwar matarsa da suke cikin motar Toyota Camry. Sauran mamatan kuma a cikin motar bus samfurin Sharron su ke.
A cewar kakakinhukumar Yan sanda DSP Kamal Datti, hatsarin ya faru ne a sanadiyar taho mu gama tsakanin motocin a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe da misalin la’asar sakaliya kuma da taimakon mutanen kauye da na jami’an tsaro aka kwaso mutanen zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, inda likitoci su ka tabbatar da mutuwar mutane goma sha uku, a yayain da sauran mutane shida su ke samun jinya.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.