Labaran siyasa ::: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

<
Abba kabir yusif PDP

A yayin da a jiya Asabar aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma kujerar 'yan majalisun dojojin na jiha, mun samu cewa tuni sakamakon zaben wasu rumfunan zabe cikin jihohin musamman na Arewacin Najeriya ya fara bayyana.
Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Rahotanni sun bayyana cewa, ba ya ga yunkurin aiwatar da magudin zabe yayin da aka cafke wata Mota makire da dangwalallun kuri'u a mazabar unguwar Magwan, an gudanar da zabe lami lafiya yayin da kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Muhammad Wakil, ya tsaya tsayin daka.
KARANTA KUMA: Zaben Kano: INEC ta ja kunnen masu yada sakamakon zaben Gwamna da Majalisar Dokoki
Kafofin watsa labarai da dama sun ruwaito cewa, ana ci gaba da gwabzawa tsakanin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP, Abba Kabir Yusuf.
Gabanin tabbatar da sahihancin wannan lamari daga bangaren hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ga yadda tiryan-tiryan sakamakon wasu rumfuna, mazabu, unguwanni da kuma wasu kananan hukumomi na jihar Kano ke ci gaba da kasancewa.
Karamar Hukumar Rimin Gado
APC 19,453
PDP 13,777
Karamar Hukumar Albasu
APC: 25,358
PDP: 18,441
Karamar Hukumar Bunkure
APC 20,407
PDP 20,222
Karamar Hukumar Madobi
APC: 24,491
PDP: 24,309
Karamar Hukumar Gezawa
PDP: 24,151
APC: 20,506
Karamar Hukumar Bebeji
Gwamna
PDP: 18,533
APC: 17,418
Majalisa
PDP: 17,830
APC: 16885
Karamar Hukumar Kibiya
PDP: 17,373
APC: 15760
Karamar Hukumar Rano
APC: 16,694
PDP: 14,992
Karamar Hukumar Ungogo
Gwamna
PDP: 42,032
APC: 26,118
No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.