Labaran siyasa :: Sakamakon zaben Adamawa APC tace bata yarda da sakamakon ba - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Sakamakon zaben Adamawa APC tace bata yarda da sakamakon ba

<
Yayin da ake ci gaba da bayyana wadanda suka lashe zaben gwamnoni a Najeriya, kawo yanzu jam'iyyar PDP ce kan gaba a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya inda aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 20 cikin 21.
A sakamakon da aka fitar na kananan hukumomin 20, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ce ke kan gaba inda ta ba jam'iyyar APC da ke mulki tazara da sama da kuri'u dubu 30.
Sai dai tuni jam'iyyar APC ta yi fatali da sakamakon zaben da ke bai wa dan takarar jam'iyyar PDP Ahmadu Umaru Fintiri zama a matsayi na gaba.
A jihar Taraba kuwa, an dakatar da karbar sakamakon zaben, har zuwa 12 na ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne yayin da hadakar 'yan sa ido, ke kiran taron manema labarai, don nuna damuwarsu game da abubuwan da suka faru a jihar na magudin zabe.
Yanzu dai lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda za ta kaya a Taraban.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.