Labaran siyasa ::: 'Ku zabi Ganduje a Kano - Takai ya bukaci magoya bayansa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: 'Ku zabi Ganduje a Kano - Takai ya bukaci magoya bayansa

<
Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nunid a cewa; dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PRP, Mallam Salihu Sagir Takai ya umarci magoya bayan sa da su zabi gwamnan jihar mai ci a yanzu, Dr Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyar APC a zaben karashe na gwamna da za'a gudanar ranar asabar, 23 ga watan Maris, 2019.
Mallam Takai ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayan sa a Kano, inda ya shaida masu cewa "Ganduje ya neme ni, mun kuma tattauna tare da cimma matsayar cewa hadaka a tsakaninmu ce kawai za ta kawo ci gaba a jihar Kano."
Bayan tabbatarwa magoya bayansa cewa akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsa da Ganduje a wannan lokaci, Takai ya kuma yi kira ga magoya bayansa na jam'iyyar PDP, "da ku fito kwanku da kwarkwatarku, ku kada kuri'unku ga gwamna Ganduje a ranar Asabar mai zuwa, 23 ga wannan watan da muke ciki."
KARANRA WANNAN : Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa
Da zafinsa: 'Ku zabi Ganduje a Kano - Takai ya bukaci magoya bayansa
A baya, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a zaben da aka kammala zagayen farko na jihar, Mallam Takai ya samu kuri'u 100,000, kuma yawan kuri'un da ake sa ran za a jefa a zabe mai zuwa ya kai kimanin 140,000.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, wacce ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Kano.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.