Labaran chikin kasa Nigeria ::: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano

<
Hukumar kwana kwana ta jihar Kano ta ce wata gobara mai karfi ta lakume wani gida a kan titin France da ke daura da bankin Zenith a yankin Sabon Gari
- Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed, ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:07 na yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Maris
- Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar ma'ajiyar iskar gas da ke a cikin wani shago da ke hade da gidan
Hukumar kwana kwana ta jihar Kano ta ce wata gobara mai karfi ta lakume wani gida a kan titin France da ke daura da bankin Zenith a yankin Sabon Gari da ke a kwaryar jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:07 na yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Maris.
"Mun samu kiran gaggawa daga jami'in rundunar 'yan sanda, Malam Kabiru Umar ( a ranar Asabar) da misalin karfe 5:07 na yamma, cewar gobara ta kama a wani gida mai shaguna a hade da shi.
KARANTA WANNAN : Da duminsa: PDP ta sha kasa a Ekiti, APC ta lashe kujeru 26 na majalisar jihar
Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano
"Jin wannan labarin ya sa muka gaggauta tura motar kwana kwana zuwa inda gobarar ta kama da misalin karfe 5:18, domin ganin an dakile yaduwar gobarar," a cewarsa.
Ya ce gobarar ta shafi dakuna guda biyar, sai falo da kuma shaguna biyar inda rahotanni suka bayyana cewa shago daya ana sayar da iskar gas.
Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar ma'ajiyar iskar gas da ke a cikin shagon.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.