Labaran chikin kasa Nigeria ::: An tattauna da masu garkuwa da mutane Wanda sukayi garko da mallam sulaiman Ahmad - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: An tattauna da masu garkuwa da mutane Wanda sukayi garko da mallam sulaiman Ahmad

<
Yanzu an kwashe mako guda tun jarrabawar da ta faru ta kama Hafizin nan na Alkur’ani mai girma Ahmed Ibrahim Sulaiman a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Kano daga jihar Kebbi a daidai yankin jihar Katsina.
Wani faifai da ya fito a yanar gizo na bayyana wadanda suke rike da shi na bukatar kudin fansa don samun sako shi da ba da tabbacin ya na halin lafiya.
Mallam Ahmed Sulaiman dai wanda shi ne mataimakin shugaban alarammomi na kungiyar JIBWIS, ya na hanyarsa ta komawa gida ne don ba da auren ‘ya’yansa mata biyu a Jumma’ar makon jiya.
Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci ci gaba da addu’a don samun sako malamin.
Kazalika Sheikh Bala Lau ya ce kungiyar ta wakilta kebantattun mutane don zantawa da wadanda ke rike da malamin.
A lokacin da Sheikh Sulaiman ya gamu da jarrabawar ya na tare da mutum biyar ciki kuwa har da wanda aka daurawa aure a bayan idon sa.
Yankin arewa maso yamma na daga yankunan da a ke samun wannan lamari na garkuwa da mutane da hakan ba ya rasa nasaba da koma bayan tattalin arziki da rashin jituwa tsakanin ma’abota tsoffin sana’o’i.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.