Labaran chikin kasa Nigeria ::: Nasarawa: PDP Za Ta Garzaya Kotu Kan Zaben Gwamna - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Nasarawa: PDP Za Ta Garzaya Kotu Kan Zaben Gwamna

<
Jami’iyyar PDP a jahar Nasarawa ta ce za ta je kotu saboda rashin gaskiya da ta ce anyi mata a zaben gwamna da aka gudanar makon jiya.
Shugaban jami’iyyar PDP a jihar Nasarawa, Francis Orogu ya ce jami’iyyar APC ta hada kai da hukumar zabe da jami’an tsaro wajen yi mata magudi a zaben.
Da yake mayar da martini, Sakataren jami’iyyar APC a jihar ta Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello ya ce suna shirye don haduwa da jami’iyyar ta PDP a kotu.
Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Nasarawa, inda wakilyar sashen Hausa ta kira lambar kakakin hukumar amma bai dauki wayar ta ba.
A bangaren jami’an tsaro kuwa, kwamandan rundunar tsaron al’umma ta Civil Defence a jihar, Muhammad Gidado Fari ya ce basu hada kai da kowa ba, sun dai bada tsaro ne don gudanar da zabe mai tsabta a jihar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.