Labaran chikin kasa Nigeria ::: Kamfanin Innoson ya rufe bankunan GT guda 7, saboda bashin da ya ke bin bankin Updated: an - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Kamfanin Innoson ya rufe bankunan GT guda 7, saboda bashin da ya ke bin bankin Updated: an

<
Kamfanin motoci na Innoson ya ce ya kulle bankunan GT guda bakwai, har sai lokacin da bankin ya mai da musu da kudin da su ke bin su kimanin naira biliyan takwas.
Mai magana da yawun kamfanin, Cornell Osigwe shi ne ya shaidawa manema labarai hakan, sannan kuma ya bayyana cewa za su kulle babbar helkwatar bankin nan da sati daya.
Yanzu-yanzu: Bankin GT ya samu matsala
Bankunan da aka rufe sun hada da guda daya a Nnewi, guda biyu a Onitsha, biyu a Awka da kuma wasu guda biyu suma a Enugu.
Kamfanin ya ce ya karbi takarda daga hannun kotu da ta ba su damar kulle bankunan har sai lokacin da bankin ya biya kudin da ake bin shi.
KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi
Sai dai kuma bankin ya yi korafi akan matakin da kamfanin ya dauka inda ya ce, hakan ya sabawa dokar Najeriya.
A karshe bankin yace za su yi iya bakin kokarin su wurin ganin sun dai-daita komai domin cigaba da aiki kamar yanda ya kamata.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.