Labaran chikin kasa Nigeria ::: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara

<
A yau Asabar, 9 ga watan Maris ne ake gudanar da zaben gwamnonin jihohin Najeriya da na yan majalisar dokokin jiha.
Don haka hukumar zabe mai zaman kanta ta tanadi akwatuna biyu daya murfinsa na da launin ja wato na zaben gwamnoni kenan yayinda na yan majalisun jihohi ke da launin baki.
A wannan babi za mu kawo maku yadda zaben ke gudana a wasu jihohi uku da suka hada da Nasarawa, Niger da kuma Kwara.
Manyan yan takarar gwamnoni a wadannan jihohin sune:
Jihar Niger:
Abubakar Sani Bello APC
Umar Nasko PDP
Jihar Nasarawa:
Mista David Ombugadu PDP
Labaran Maku APGA
Abdullahi Sule APC
Jihar Kwara:
Abdulrahaman AbdulRasaq APC
Barr. Razak Atunwa PDP
Rashin zuwan wakilan jam'iyyu ya sa ba a fara tantance masu zabe ba a wata makarantar Firamari da ke birnin Lafiya a jihar Nasarawa.
Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara
A yanzu haka jirgin rundunar sojin saman Najeriya mai saukar ungulu na rangaji a jihar Kwara domin kula da lamarin tsaro.
A kokarin da hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ke yi na hana sayan kuri'a, hukumar ta yi nasarar damke wani mai suna Abdulkareem Abdulsalam a ya yin da yake raba kudi a ranar zabe a jihar Kwara.
EFCC Nigeria
@officialEFCC
#Polls Operatives of the EFCC Ilorin Zonal Office, Kwara State arrest Abdulkareem Abdulsalem for sharing money to voters on election day at Unit 7, Kwara State College of Education.
#SayNoToVoteBuying
128 10:10 AM - Mar 9, 2019
93 people are talking about this
Source: Hausa.legit.ng

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.