Labaran chikin kasa Nigeria ::: ja wabin shugaba Buhari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: ja wabin shugaba Buhari

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya sake lashe zabe a wa’adi na biyu, ya ce zangon mulkinsa na karshe zai zamanto mai tsauri, kamar yadda rahotanni da dama suka nuna.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da ya yi da majalisar zartarwarsa a karshen makon nan.
Shugaban wanda ya lashe zabe karkashin jam’iyyar APC, ya ce zai tabbata ya cika alkawuran da ya yi naganin tsaro ya tabbata da bunkasa tattalin arzikin kasar tare da yaki da cin hanci da rashawa.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Sakataren gwamatin tarayya, Boss Mustapha da ministoci da dama.
A ranar Asabar da ta gabata aka gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, inda Buhari ya doke abokin hamayyarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.