Labaran chikin kasa Nigeria ::: An Hana Zirga-Zirga Ranar Zabe A Plato - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: An Hana Zirga-Zirga Ranar Zabe A Plato

<
Rundunar ‘yan sandan jahar Pilato ta sanya dokar hana yawo a duk fadin jahar yayin gudanar da kammala zaben gwamna da za’a yi a rumfuna arba'in na kananan hukumomi tara na jahar Pilato.
Wata sanarwa dake da sanya hannun kakakin rundunar ‘yan sandan na jahar Pilato. DSP, Tyopev Terna, tace dokar hana zirga-zirgan zata fara aiki ne daga karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamman ranar Asabar.
Sanarwar tace daukan matakin ya zamo tilas saboda a ba jama’a dammar gudanar da zaben wanda suke so ba tare da wata musgunawa ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.