Labaran chikin kasa Nigeria ::: Da duminsa: An nemi ma'aikatan INEC an rasa a rumfar zaben Tinubu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Da duminsa: An nemi ma'aikatan INEC an rasa a rumfar zaben Tinubu

<
Jami'an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da ma'aikatan wucin gadi na hukumar ba su iso rumfar zaben jagora a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Ahmed Tinubu ba har karfe 10 na safiya duk da cewa karfe takwas ya dace a fara zabe.
Rumfar zaben ita ce mai lamba 047 da ke gunduma ta 3 a karamar hukumar Ikeja na jihar Legas kamar yadda Sahara reporters suka ruwaito.
Babu jami'an INEC kuma babu 'yan yiwa kasa hidima wato NYSC da hukumar ke dauka a matsayin ma'aikatan wucin gadi har zuwa karfe 10 na safiya.
DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi
Da duminsa: An nemi ma'aikatan INEC an rasa a rumfar zaben Tinubu
A halin yanzu dai hukumar ta INEC ba ta bayar da wani dalilin jinkirin ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.