Labaran siyasa ::: ziyara mai girma shugaban kasa Nigeria xuwa kano - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: ziyara mai girma shugaban kasa Nigeria xuwa kano

<
Dazu da maraice shugaban Najeriya ya kammala ziyarar yakin neman zabe a Kano, sai dai shugaban bai yi wani sabon alkawari ba musamman ta fuskar lamuran da suka shafi farfado da masana'antun Kano da harkokin kasuwanci.
Gabanin bayyana a dadalin taron, sai da shugaban ya bude wata gada da gwamnatin Kano ta gina a daf da Barikin sojoji na Bokavo kuma ya kai ziyarar neman tabarraki fadar mai martaba sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi na biyu.
Dubbun dubatun mutane ne suka yi dafifi domin tarbar shugaban, sai dai a iya cewa taron ya saba da wadda aka saba gani a lokutan baya, inda Kano kan tsaya cik har sai shugaban ya kammala ziyara.
A wannan karon jama'a da dama musamman a sassa daban daban na birnin Kano sun ci gaba da harkokin su.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.