Labaran siyasa :::: Dalilin da yasa muka yi watsi da Buhari muka kama Atiku – Kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :::: Dalilin da yasa muka yi watsi da Buhari muka kama Atiku – Kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa

<
Kungiyar masu ruwa da tsaki na arewa wato Northern Stakeholders Forum (NSF), ta bayar da dalilan da suka sanya ta yin watsi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta zabi dan takarar shugban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaben Shugaban kasa da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Da suke jawabi a taron yanki da aka gudanar a Mambayya House da ke Kano, Aminu Adam, daraktan kungiyar ya bayyana cewa sun marawa Atiku baya ne saboda shugaba kasa Buhari ya ba yan Najeriya kunya.
Ya kara da cewa suna daga cikin matasan da suka jagoranci zanga-zanga a Amurka, okacin da suka yi zargin PDP na kokarin magudi a zaben 2015, wanda ya nuna Bhari yafi Dr Goodluck Jonathan kari, inda yayi kira ga kasashe duniya da su mayar da hankali sosai aka zaben don tabbatar da nasarar Buhari.
Dalilin da yasa muka yi watsi da Buhari muka kama Atiku – Kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa
Sanan yace lokaci da Buhari yah au mulki, sai suka lura cewa ya gaza cika alkawaran kamfen dinsa, musamman a fannin yaki da cin hanci da rashawa, tattalin arziki da kuma tsaro.
A nashi jawabi babba bako na mussamman a taron, Alhaji Nastura Nasir Sharif ya bayyana cewa Buhari ba mutum bane mai tsayawa akan maganganunsa.
KU KARANTA KUMA: APC zuwa PDP: Jaruma Maryam Gidado tayi kaca-kaca da masu sukar Adam A. Zango
A cewar Sharif, Buhari na ikirarin ya yaki cin hanci da rashawa, amma daga baya ya tabbatar da cewa akwai son kai a yakin sannan shi kansa yaa tattare da barayin yan siyasa da ke fuskatar tuhuma a hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).
Yace a halin yanzu Atiku ne mafita ga arewa domin zai fi Buhari tabuka abun arziki.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.