Labaran siyasa ::: Banyi nadamar goyon bayan Abacha ba - Dan takarar shugabancin kasa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Banyi nadamar goyon bayan Abacha ba - Dan takarar shugabancin kasa

<
- Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ID, Edozie Madu yana daga cikin wadanda suke goyon bayan tsoshon shugaban soji, Sani Abacha
- Madu ya ce bai yi nadamar goyon bayan Abacha ba saboda niyyarsu shine ya rikide zuwa farar hula kuma ya kawo canji a Najeriya
- Dan takarar shugabancin kasar kuma ciyaman na jam'iyyar ta ID ya yi tsokaci a kan wasu batutuwa da ke faruwa a Najeriya a yanzu
Dan takarar shugabancin kasa kuma shugaban jam'iyyar Independent Democrats (ID), Edozie Madu ya bayyana yadda ya marawa tsohon shugaban kasar mulkin soja, Sani Abacha baya a yunkurinsa na komawa dan takarar shugaban kasa na farar hula a 1998.
Madu ya yi wannan jawabin ne a hirar da ya yi da Premium Times inda ya yi tsokaci kuma a kan wasu batutuwa da ke faruwa a Najeriya da suka hada da zabe, samar da 'yan sandan jihohi, yakin aikin ASUU da batun albashi mafi karanci.
Banyi nadamar goyon bayan Abacha ba - Dan takarar shugabancin kasa
DUBA WANNAN: Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC (jerin sunaye da mukamai)
Da aka tambaye shi ya fadi rawar da ya taka a zamanin mulkin soja na Abacha, Madu ya amsa da cewa:
" Ina daya daga cikin wadanda suke goyon bayan tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ya dawo kan karagar mulki a 1997. Amma sai Abacha ya rasu shi yasa hakan bai yiwu ba, niyyar mu shine tabbatar da cewa Abacha ya kawo sauyi a Najeriya a matsayinsa na shugaban mulkin farar hula.
"Tun daga wannan lokacin, ana ta dama wa da ni a siyasa. Ina cikin jam'iyyar PDP tun 1999 kafin wannan lokacin ni ne shugaban kungiyar matasan tarayyar Najeriya a 1998.
"Ina jam'iyyar PDP a lokacin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ke mulki kafin na bar jam'iyyar a 2011. Na kuma zama shugaban jam'iyyar siyasa ta Congress for Democratic Change (CDC). A 2013 mun kafa jam'iyyar Independent Democrats kuma muka yiwa jam'iyyar rajista a 2013. Muna da mambobi miliyan 3.2 kuma kashi 68 cikin 100 matasa ne masu shekaru 25 zuwa 40. "
Madu ya ce idan ya zama shugaban kasa zai rushe fifikon da ake bawa 'yan asalin jihohi kuma ya gamsu da shirin INEC na gudanar da zabe sannan ya ce baya goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi domin gwamnoni za su rika amfani da su ta hanyoyin da basu dace ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.