Labaran siyasa ::: Atiku ya shahara, sai dai nasara ta na ga Buhari - Eurasia Group - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Atiku ya shahara, sai dai nasara ta na ga Buhari - Eurasia Group

<
Yayin da rage sauran kwanaki shida kacal a gudanar da babban zabe na kujerar shugaban kasa, wata kungiyar duniya da ta shahara akan kiyasi da nazarin siyasa, ta bayyana hasashen ta dangane da wanda zai yi nasara a zaben bana.
Kungiyar Eurasia Group, da ta shahara a matsayin mafi kololuwar kungiya mai kiyasi da nazari akan siyasa, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zamto zakara wajen samun nasara yayin zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.
Sakamakon kididdigar karshe da kungiyar ta fitar bayan kiyasi da nazarin siyasa bisa ga jagorancin shugaban ta, Ian Bremmer, ta ce shugaban kasa Buhari zai yi nasara da kaso sittin cikin dari a babban zabe na bana.
Buhari yayin taron sa na yakin neman zabe a jihar Kebbi
Bremmer dan kasar Amurka, zakakuri akan ilimin siyasa wanda ya kafa kungiyar Eurasia tun a shekarar 1998, ya ce ko shakka ba bu dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu mashahuranci na gaske cikin 'yan makonnin da suka gabata.
Sai dai Bremmer ya ce duk da wannan mashahuranci, Buhari zai yi galaba a kansa bisa ga wasu dalilai ka ma daga yadda jam'iyyar APC ke jagorancin jihohi 23 na Najeriya duba da na PDP mai jihohi 13 kacal.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, kungiyar Eurasia ta yi hasashen yadda shugaba Buhari zai nasara akan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, makonni kadan gabanin babban zabe na 2015.
KARANTA KUMA: 'Kaddara ta riga fata: Miji na ya zama shugaban kasa - Titi Abubakar
Kazalika kungiyar ta ce hukuncin da shugaban kasa Buhari ya dauka wajen dakatar da alkalin alkalai na Najeriya, Justice Walter Onnoghen, ba zai yi tasiri ba wajen rinjayar da sakamakon zaben bana.
Baya ga rashin samun magoya baya 'yan gani kashe ni tamkar na Buhari, kungiyar ta ce jagororin yakin neman zabe na PDP ba za su yiwa Atiku yakin neman zaben sa ba tuburan kuma haikan sakamakon yadda suke hankoron samun nasarar na su kujerun na siyasa

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.