Labaran siyasa ::: Ana wata gawata. Shugaban PDP ya soki Buhari game da gayyatar gwamnonin kasar Nijar taronsa a Kano - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Ana wata gawata. Shugaban PDP ya soki Buhari game da gayyatar gwamnonin kasar Nijar taronsa a Kano

<
Jam’iyyar PDP ta soki lamirin jam’iyyar APC na gayyatar gwamnonin kasar Nijar guda biyu zuwa halartar gangamin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari daya guda a jahar Kano a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu.
Gwamnonin kasar Nijar da suka hada da Gwamna Issa Moussa na jahar Zinder, da Gwamna Zakiri Umar na jahar Maradi sun samu damar halartar yakin neman zaben shugaba Buhari daya gudana a filin wasanni na Sani Abacha.
KU KARANTA: Dalibai Musulmai sun yi barazanar mamaye jahar Legas akan bahallatsar Hijabi
Ganduje da Gwamnonin
Hadimin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, akan harkokin kafafen sadarwar zamani, Salihu Tanko Yakasai ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter, inda yace gwamnonin biyu sun halarci taron ne da nufin mara ma shugaba Buhari baya.
Sai sai shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya bayyana halartar gwamnonin da shirin sayar da Najeriya shugaban kasa Buhari ke yi ta hanyar dauko Sojojin haya daga kasashen ketare da nufin su kada masa kuri’a a zaben ranar 16 ga watan Feburairu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Secondus yana kira ga kasashen duniya dasu sanya idanu da kyau game da wannan shiri na jam’iyyar APC, inda ya kara da cewa zabe aikine na yan kasa, don haka bai ga dalilin da wasu gwamnonin kasar waje zasu je Kano da nufin tarbar Buhari a kasarsa ba.
“Mun dade muna fada shugaba Buhari ba shi da kyakkyawar manufa akan Najeriya, shugaban ya sayar da kasar ga wasu mutane na daban da yafi kauna fiye da yan Najeriya, halartar gwamnonin kasashen waje guda biyu ya nuna APC na shigo da jama’a daga kasashen waje don halartar tarukansu.
“Allah Ya tona asirinsu, na ji dadi, kun san Buhari na fadi hatta har a jihohin da bashi da masoya wai zai ci zabe, zai lashe kuri’un jahar, daga cikin hanyoyin da yake shirin cimma wannan buri shine ta shigo da bakin haure da zasu zabeshi, kuma yara kanana.” Inji shi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.