Labaran Duniya ::: shin ko kunsa dalilinsa na soke zuwa Tsohon shugaban kasar Amurka ya soke ziyarar da zai kawo Nigeria - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya ::: shin ko kunsa dalilinsa na soke zuwa Tsohon shugaban kasar Amurka ya soke ziyarar da zai kawo Nigeria

<
Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton ya soke ziyarar da ya shirya kawowa Nigeria gabanin babban zaben kasar da za a gudanar ranar Asabar
- Mr Clinton ya ce ya soke ziyarar ne saboda gudun kar duniya ta kali wannan ziyarar a matsayin wata hanyar tsoma hannu a zaben kasar
- Gidauniyar Kofi Annan tare da hadin guiwar kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) suka shirya wannan ziyara da Mr Clinton zai kawo kasar
Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton ya soke ziyarar da ya shirya kawowa Nigeria gabanin babban zaben kasar da za a gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, yana mai cewa duniya na iya kallon wannan ziyarar a matsayin wata hanyar tsoma hannu a siyasar kasar.
A baya dai an shirya cewa Clinton zai kawo ziyara Nigeria, inda zai sauka a babban birnin tarayya Abuja, tare da Baroness Patricia Scotland, babbar sakatariyar kungiyar kasashen rainon Burtaniya, "Commonwealth."
Gidauniyar Kofi Annan tare da hadin guiwar kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) suka shirya wannan ziyara da Mr Clinton zai kawo kasar.
KARANTA WANNAN: Da duminsa: EFCC ta cafke Babachir Lawal, za ta gurfanar da shi yau kan zargi handame N544.1m
Ta leko ta koma: Tsohon shugaban kasar Amurka ya soke ziyarar da zai kawo Nigeria
"Duba da abubuwan da suka faru a cikin kwanakin da suka gabata, kuma bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, ya zama tilas ga tsohon shugaban kasar Amurka, Mr Clinton ya soke ziyarar da ya shirya kawowa Nigeria domin gujewa cece-kucen jama'a da zargin ko akwai siyasa a ciki, sabanin manufofin kwamitin. A don haka, ba zai zo Abuja ba," a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun Clinton, Angel Urena.
Clinton, a cewar sanarwar, zai ci gaba da goyon bayan kwamitin NPC domin ganin cewa an gudanar da sahihin zabe a Nigeria.
An shirya cewa zai gabatar da jawabi a bukin taron sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kwamitin NPC ya shiryawa 'yan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyun siyasa na kasar.
Sanarwar ta c daga bisani kuma an shirya Clinton zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke neman tazarcen kujerarsa, da kuma babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.