Labaran Duniya. ::: Macedonia ta Santa hannu akan Neman shiga nato - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya. ::: Macedonia ta Santa hannu akan Neman shiga nato

<
Macedonia ta rattaba hannu kan wata takarda ta hanyar neman shiga rundunar tsaro ta tarayyar Turai, wato NATO.
Macedonia ta rattaba hannu kan wata takarda ta hanyar neman shiga rundunar tsaro ta tarayyar Turai ta NATO, a karkashin wani tsarin da za’a iya kammala shi nan da zuwa shekara mai zuwa.
Babban Sakataren NATO Janar Jens Stoltenberg da Ministan harakokin tsaro na Macedonia Nikola Dimitrov sun kasance daga cikin wadanda suka halarci bikin sa-hannun yau Laraba a Brussels.
Stoltenberg ya ce, kara Macedonia don ta zama kasa ta 30 a kungiyar NATO, zai kawo zaman lafiya da tsaro ga yankin baki daya.
Da yake tsaye a kusa da Stoltenberg, Dimitrov ya ce abin da ke da muhimmanci ga kasarsa ta shiga wannan yarjejeniya ita ce "ba za’a barta a baya ba."
Daman kasar Girka ce ta toshe yunkurin Macedonaia na shiga kungiyar tsaron ta NATO, saboda rigimar da suka yi shekaru suna yi, a kan sunan “Macedonia” din, wanda suna ne da wani yanki da Girka yake anfani da shi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.