Labaran chikin kasa Nigeria ::: Rikicin Obasanjo da Buhari: Gwamnan jahar Kaduna yayi karin haske - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Rikicin Obasanjo da Buhari: Gwamnan jahar Kaduna yayi karin haske

<
Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai yayi karin haske game da rikicin daya shiga tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, sai dai yace alakar mutanen biyu ta wuce saninsa.
El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yace alaka tsakanin Buhari da Obasanjo tsohuwar alaka ce data faro tun daga shekarar 1975 zamanin mulkin Soja, inda dukaninsu mambobi ne a majalisar koli ta Soja.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun kashe Malamin jami’a, sun yi awon gaba da guda 2
Obasanjo, Buhari da El-Rufai
Haka zalika gwamnan, wanda kowa ya sanshi da Obsanjo ya kara da cewa ko a shekarar 196-1978 Obasanjo ya nada Muhammadu Buhari a matsayin ministan albarkatun man fetir, a zamanin da yake shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja.
“Alakar mutanen nan biyu ta faro tun kafin na sansu ko su san ni, don haka da wuya wani yace maka ya san tsakaninsu ko kuma zai shiga tsakaninsu. Na san duka sosai, nayi aiki da Obasanjo, kuma na fahimceshi iya gwargwado kuma shima ya karanceni iya gwargwado, haka shima Buhari.
“Sai dai abinda nake ganin ya kunno rikici a tsakaninsu shine bambamcin abinda Obasanjo yake tsammani daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma abinda shi shugaba Buhari yake ganin zai iya yi.” Inji El-Rufai.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya nanata ra’ayinsa na cewa yana da fahimtar Buhari da Obasanjo sun yi hannun riga ne musamman saboda zaton da tsammanin da Obasanjo ke dasu daga mulkin gwamnatin Buhari, amma sai Buhari ya saba masa saboda shi kuma yana da irin ra’ayinsa game da yadda ya kamata a tafiyar da mulki.
Sai dai duk da wannan rikici dake tsakanin Obasanjo da shugaba Buhari, El-Rufai na ganin Buhari zai samu nasara gagaruma a zaben 2019, inda yace ayyukan da Buhari ya gudanar su zasu sanya jama’a su bashi kuri’un da yake nema domin zarcewa akan mukaminsa.
Daga karshe gwamnan yayi kira da yan Najeriya dasu yi duba da halin da Najeriya ke ciki a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma halin da za ta kasance idan ya zarce, sa’annan su duba halin da kasar ke ciki a yanzu, ta haka ne zasu fahimci aikin da Buhari ya yi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.