Labaran chikin kasa Nigeria :::: Ra'ayoyin Jama'a Akan Shirin Shugaba Buhari Na Kai Najeriya Mataki Na Gaba - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :::: Ra'ayoyin Jama'a Akan Shirin Shugaba Buhari Na Kai Najeriya Mataki Na Gaba

<
Bayan karbar takardar shaidar lashe zabe karo na biyu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nanata cewa taken yakin neman zaben sa “NEXT LEVEL” wato mataki na gaba da gwamnatin sa za ta dauka zai tabbata.
Matakin kuwa ba mamaki kamar yadda ya ambata ya hada da sanya hannun kowa cikin gwamnatin, da kuma gargadi ga tsokanar abokan hamaiya ko ma jigon 'yan adawa, Atiku Abubaakar da ya ce su na da abu iri daya wato muradin ci gaban Najeriya duk da bambancin ra’ayin da ke tsakanin su.
Janar Buba Marwa da ke cikin masu karbar sakamako na shugaba Buhari ya yi karin bayani akan wannan mataki na gaba da ya hada da abin da ba a kammala a baya ba musamman lamarin tsaro.
Mutane da a ka zanta da su na fatar samun garambawul a mukaman gwamnatin don kawo mafi kwarewar jami’ai a bangarori daban-daban.
Yanzu dai za a jira a ga inda alkiblar gwamnatin za ta karkata gabanin sake rantsar da shugaban a ranar 29 ga watan Mayu.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.