Labaran chikin kasa Nigeria :: Me ya sa INEC ta dage zaben Najeriya? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: Me ya sa INEC ta dage zaben Najeriya?

<
Hukumar zaben ta Najeriya ta ce ta dage zaben ne zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
Da yake sanar da matsayin hukumar ranar Asabar da kusan asubahi, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni zuwa ranar tara ga watan Maris.
Farfesa Yakubu ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalolin rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar a kan lokaci.
A cewarsa, "Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta gana ranar Juma'a, 15 ga watan Fabrairu inda ta sake nazari kan shiriye-shiryenta na zaben shekarar 2019, don haka an dage zaben da za a yi ranar Asabar 16 ga watan Fabairu zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Kazalika, za a gudanar da zaben gwamnoni ranar tara ga watan Maris."
Matsayin INEC bai sauya ba kan rikicin APC a Zamfara
Yadda ake shirye-shiryen zaben Najeriya
Da ma dai rahotanni daga sassan kasar da dama sun bayyana cewa ba a kai kayan aikin zaben ba har cikin dare, abin da ya sa wasu 'yan siyasa zargin cewa ana shirya magudi.
Masu sharhi na ganin wannan mataki zai kara tabbatar da zargin da wasu suka yi ta yi cewa hukumar ba ta shirya ba, amma ta rinka musanta hakan.
Hakan kuma ka iya haddasa rashin jin dadi a tsakanin wasu 'yan kasar ganin yadda da ma suka yi tattaki zuwa yankunansu domin kada kuri'a.
Martani
Tuni dai 'yan siyasa suka fara mayar da martani inda kwamitin yakin neman zabe na Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da matakin na INEC, sannan suka yi kira ga magoya bayansu da ka da su yi kasa a gwuiwa.
A sakon da ya aike wa manema labarai, mai magana da yawun kamfe din Festus Keyamo, ya kuma zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yunkurin kawo tsaiko ga zaben, sai dai babu wata hujja da ya gabatar.
Sai dai mai magana da yawun PDP, Kola Ologbondiyan ya ce jam'iyyarsu ta yi matukar kaduwa da jin labarin dage zaben.
"Wannan dage zabe wata kutunguila ce da aka shirya domin ceto Shugaba Buhari daga kayen da yake shirin sha amma ba za ta yi tasiri ba", in ji Mr Kola.
Kawo yanzu jam'iyyar PDP ba ta mayar da martani kan dage zaben ba.
Wannan shi ne karo na uku a jere da ake dage zaben Najeriya bayan da hakan ta faru a shekarun 2011 da 2015 da kuma bana.
Sharhi, Naziru Mikail, BBC Abuja
Sanarwar hukumar zaben ta kada zukatan 'yan kasar da dama, kuma za ta jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin manyan jam'iyyun kasar, domin babu shakka kalaman na Farfesa Yakubu ba za su gamsar da dama daga cikin 'yan Najeriya ba.
Wani abu da zai kara bakantawa mutane rai shi ne yadda hukumar ta shafe shekara hudu tana shirya wannan zabe, amma kwatsam sai a mintinan karshe ta sauya matsaya.
Gabanin zaben dai gobara ta tashi a wasu ofisoshin hukumar amma ta dage cewa hakan ba zai shafi shirnta na zabe, kuma a yanzu ba ta ambaci hakan a matsayin dalili ba.
Sai dai tambayar a nan ita ce, mai ya sa sai yanzu, mai ya hana hukumar fitowa ta bayyana matsayinta tun farko, kuma mai ya sa ba ta dauki darasi daga ayyukanta na baya ba.
Jama'a da dama sun kashe kudade, wasu sun bar ayyukansu, wasu sun yi doguwar tafiya domin zuwa wuraren da za su kada kuri'unsu. Wannan mataki zai bakanta musu rai.
Wasu na hasashen wannan dagewar ka iya shafar adadin mutanen da za su fito domin kada kuri'unsu a mako mai zuwa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.