Labaran chikin kasa Nigeria ::: Mai zaku iya cewa dagane da daga zabe ra'ayoyin wasukenan - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Mai zaku iya cewa dagane da daga zabe ra'ayoyin wasukenan

<
Kawo yanzu dai kusan a iya cewa ba labari bane batun dage zaben gama-gari na Najeriya da za'a gudanar a da yau Asabar har sai zuwa ranar Asabar mai zuwa kamar dai yadda shugaban hukumar zaben mai zaman ta ta kassa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyanawa duniya.
Sai dai tun bayantabbatar hakan, yan Najeriya ke cigaba da bayyana ra'ayoyin su akan hakan inda wasu ke goyon bayan hukumar ta INEC kan matsayar da ta dauka musamman ma idan akayi duba da matsaltsalun da ka iya tasowa idan har aka dage sai an gudanar da zaben.
Rayukan wasu sun baci, wasu kuma sunyi murna; ra'ayoyin 'yan Najeriya game da da dage zabe
KU KARANTA: Daurawa ya jagoranci malamai sama da 100 zuwa wurin Kwankwaso
A hannu daya kuma wasu na ganin hakan tamkar kunyata Najeriya ne da kuma 'yan Najeriya a idon duniya. Wasu kuma ma na ganin cewa zaben zai samu karancin masu kada kuri'a musamman ma duba da yadda mutane suka kashe kudaden su wajen zuwa inda za suyi zabe.
Tun farko dai mun kawo maku labarin cewa hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Na Kasa (INEC) ta dage babban zaben 2019 saboda kalubalen da ta fuskanta a wurin rabon kayayakin zabe zuwa wuraren da za ayi amfani da su.
Sanarwar dagewar ta fito ne daga bakin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu misalin karfe 2.45 na safiyar Asabar 16 ga watan Fabrairu bayan ya kammala taron gaggawa da hukumomin tsaro da masu sanya ido a kan zabe da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce ba zai yiwa a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara da farko ba hakan ya tilasta aka dage zaben da mako daya.
A yanzu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu yayin da zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi kuma za ayi a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.