Labaran chikin kasa Nigeria :: mai yayi zafi wasu matasa sun kona wata mata a arewachin Nigerian - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: mai yayi zafi wasu matasa sun kona wata mata a arewachin Nigerian

<
Wasu fusatattun matasa sun kona wata mata da ranta a garin Nasarawan Eggon
- Lamarin ya afku ne bayan wasu kananan yara sun taso daga makarantar Boko sai matar cikin shiga na mahaukata ta ja daga cikinsu
- Hakan ya sa shakku a zukatan mutanen da ke wajen domin dama yankin na fama da matsalar sace-sacen mutane sannan kuma babu alamu da ke nuna cewa matar mahaukaciyar gaske ce
Rahotanni sun kawo cewa a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu wasu fusatattun matasa sun kona wata mata da ranta a garin Nasarawan Eggon. Lamarin ya afu ne a kusa da ofishin hukumar tsaro na farin kaya, da misalin karfe 1:00pm.
An tattaro cewa a yayinda wasu kananan suka taso daga makarantar Boko, si matar ta ira daya daga cikinsu sannan ta ja shi gefe.
Matasa sun kona mace da ranta a wata jihar Arewa
Lokaci guda sai hankalin mutane ya tattara a kanta, sakamakon yanayi da tayi da mahaukat, kana ganin siffanta ka ga na mahaukaciya. Amma mutane sun lura da cewar babu alamar hauka a tare da ita, kawai dai shigarta ne yayi na mahaukata sannan kuma ya zo daidai da halin da al’umman garin Nasarawan Eggon, suke ciki na fama da sace-sacen yara kanana.
Hakan ya sanya suke zargin ire-iren wadannan mahaukatan saboda duk da cewa ita a siffar mahaukata take, amma tana amsa wayar salula na hannu.
KU KARANTA KUMA: 2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP
Kiran yaron da ta yi zuwa wani lungu, sai ya sa Jama’a yin ca a kanta, duk da cewa shedun gani da ido sun ce a lokacin da aka kamata da yaron ta fara magana cewa ba ita kadai ba ce, ta fara jawabi amma zuwan wasu jama’an suka afka mata da duka da sanya wuta nan take ta yi kasa.
Duk da kokarin da jami’an tsaron (NSCDC) suka yi domin su cece ta a hannun matasan amma abin ya ci tura har sai da suka kona ta.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.