Labaran chikin kasa Nigeria ::: An kama manyan barayi 2 dauke da muggan bindigogi 4 a garin Gusau - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: An kama manyan barayi 2 dauke da muggan bindigogi 4 a garin Gusau

<
Mafusatan matasa a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara sun kone wasu mutane biyu da ake zargi da safarar muggana bindigogi da ransu da marecen ranar Juma'ar da ta gabata a unuwar Dallatu kusa da babbar kasuwar garin.
Majiyar mu dai ta bayyana mana cewa tun farko wasu matasa ne suka lura da bindigogin har hudu kirar AK47 a cikin motar mutanen kirar Golf ja wanda nan take kuma suka ankarar da jama'a kan hakan.
Da dumin sa: An kama manyan barayi 2 dauke da muggan bindigogi 4 a garin Gusau
KU KARANTA: Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan dage zaben da INEC tayi
Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa tona masu asirin da matasan suka yi ke da wuya sai kamai al'ummar gari suka far masu inda suka dauki doka a hannun su ta hanyar kona su da ran su tare da motar da suke ciki.
Majiyar mu dake a garin Gusau din dai ta tabbatar mana cewa jami'an tsaron farar hula da 'yan sanda sun kasa hana matasan aiwatar da aniyar su sai dai suka tsaya daga nesa suna kallon su kafin daga bisani su kwaci daya zuwa chaji ofis.
Jihar dai ta Zamfara da ma wasu sassa na jihohin dake makwaftaka da su kamar Katsina da Sokoto na fama da rashin tsaro na sace sace da kuma garkuwa da mutane domin kudin fansa, lamarin da ya addabi al'umma sosai.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.