Labaran chikin kasa Nigeria :: Ipman ta umarchi Mambinta su rage farashin mai - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: Ipman ta umarchi Mambinta su rage farashin mai

<
 wani mataki na kwadaitar da ‘yan Najeriya su fita zabe a ranar Asabar mai zuwa, kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta a Najeriya, IPMAN, ta ba mambobinta umurnin su rage farashin man.
Kungiyar ta IPMAN, ta nemi mambobinta su rage farashin man daga N145 zuwa N140, kamar yadda jaridun Najeriya da dama suka ruwaito.
Wannan mataki a cewar kungiyar, ya biyo bayan yanayin da aka shiga na siyasa, bayan da INEC ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, duk da cewa ‘yan Najeriya sun shirya tsaf.
IPMAN ta yanke shawarar rage N5 daga farashin mai N145 ne da zimmar karawa ‘yan Najeriya kwarin gwiwar fita zabe a karshen mako kamar yadda rahotannin suka nuna.
Ta ce matakin zai fara aiki ne daga ranar 20 zuwa 25 ga watan nan na Fabrairu.
“Muna kira ga mambobinmu da su amsa wannan kira na rage farashin daga N145 kan lita daya zuwa N140.” Inji wata sanarwar da jaridun Najeriya suka ruwaito dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Chinedu Okworonkwo.
'Yan Najeriya da dama sun yi tafiye-tafiye a sassan kasar domin zuwa inda za su kada kuri'unsu a karshen makon da ya gabata, amma hukumar zabe ta dage zabe inda ta ce ta fuskanci wasu matsaloli da suka shafi jigilar kayayyakin zabe.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.