Labaran chikin kasa Nigeria :: An Hallaka wakilin zabe a Bihar taraba - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: An Hallaka wakilin zabe a Bihar taraba

<
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun hallaka wasu wakilan zabe a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun hallaka wasu wakilan zabe wato "Agents" na jam’iyar APC a jihar Taraba, ciki harda wani na hannun daman dan takarar gwamna na jam’iyar APC Sani Abubakar Danladi.
Kuma an yi musu kwantar bauna ne, lokacin da suke raka sakamakon zabe zuwa cibiyar hada sakamakon watau "Collection Centre" na mazabar Amar, dake cikin karamar hukumar Karim Lamido, a arewacin jihar.
Mr Aron Arthimas dake zama kakakin jam’iyar APC a jihar, ya ce sun kadu da wannan tashin hankalin.
To sai dai kuma, kawo yanzu rundunan 'yan sandan jihar Taraban, ta bakin kakakinta David Misal, ta ce ba zata kyale ba.
Kawo yanzu haka ma dai ana cigaba da hada hancin sakamakon zaben dake fitowa daga kananan hukumomi, yayin da sai a yau ne za’a gudanar da zaben a wasu yankuna na jihar Taraba, sakamakon tangardar da aka samu a jiya

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.