Labaran chikin kasa Nigeria :::: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da hadimin gwamna Udom Emmanuel - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :::: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da hadimin gwamna Udom Emmanuel

<
- Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewa Keftin Iniobong Ekong (mai ritaya). hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan harkokin tsaro
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton sojoji ne suka yi garkuwa da Ekong a daren ranar Asabar
- Sai dai rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu ba ta samu wani korafi kan sace hadimin gwamnan ba, amma zata kaddamar da bincike kan hakan
Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewa an yi garkuwa da babban mashawarcin gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan harkokin tsaro na jihar, Keftin Iniobong Ekong (mai ritaya).
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton sojoji ne suka yi garkuwa da Ekong a daren ranar Asabar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Akwa Ibom wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an yi garkuwa da Keftin Ekong tare da tsare shi a wani boyayyen waje da ba a san ko ina ba ne a garin Fatakwal.
KARANTA WANNAN : KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato
Da duminsa: Ana tsakiyar zabe, an yi garkuwa da hadimin gwamna Udom Emmanuel
Da aka tuntube shi, jami'in hulda dajama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Mr Odiko McDon ya ce har yanzu rundunar 'yan sanda bata karbi wani korafi kan sace hadimin gwamnan ba. Sai dai ya yi alkawarin cewa rundunar zata kaddamar da tuntuba tare da daukar mataki.
A wani labarin, an kammala rarraba kayayyakin zabe a wasu rumfunan zabe na garin Uyo, babban birnin jihar a yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara tantance masu kad'a kuri'a da kuma fara zabe.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.