Labaran chikin kasa Afrika ::: Al Shabab Ta Dauki Alhakin Harin Mogadishu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Afrika ::: Al Shabab Ta Dauki Alhakin Harin Mogadishu

<
Masu kamfanin rukunin motocin jigilar majinyata na Aamin sun fada wa ‘yan jarida cewa sun dauko gawarwaki a kalla 9, ciki har da na wasu mata uku.
Kungiyar mayaka ta al-Shabab mai tsattsauran ra’ayin addini ta yi ikirarin kai wasu hare-hare biyu a Somalia jiya Litini, inda mutane akalla 9 su ka mutu.
An kai harin ne da bam da aka saka a cikin mota a tsakiyar birnin Mogadishu, sannan kuma aka harbe wani mutum a wata tashar jirgin ruwa a yankin Puntland mai kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kai.
Masu kamfanin rukunin motocin jigilar majinyata na Aamin sun fada wa ‘yan jarida cewa sun dauko gawarwaki a kalla 9, ciki har da na wasu mata uku.
Sannan sun yi jigilar wasu mutane 7 da su ka ji raunuka. Haka zalika, wasu majiyoyin tsaro sun gaya ma Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa an hallaka wani babban jami’in tsaro a wannan harin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.