Labaran afirka. :::: Bam Ya Halaka 'Yan sanda a Masar - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran afirka. :::: Bam Ya Halaka 'Yan sanda a Masar

<
‘Yan sandan biyu na bin mutumin ne wanda ke dauke da wani abu mai fashewa, wanda ya tarwatse a kusa da Masallacin Al Azhar.
Wasu ‘yan sandan kasar Masar biyu sun rasa rayukansu bayan da wani abin fashewa ya tarwatse a hannun wani mahari da suke bi a tsakiyar birnin Alkahira.
Mutumin ya mutu sannan wasu mutum uku sun jikkata.
Jami’an tsaro sun ce ana zargin maharin da laifin yunkurin kai harin bam akan ‘yan sanda a birnin na Alkahira a makon da ya gabata.
‘Yan sandan biyu na bin mutumin ne wanda ke dauke da wani abu mai fashewa, wanda ya tarwatse a kusa da Masallacin Al Azhar.
A ranar Juma’a aka zargi mutumin da yunkurin dasa bam a birnin Alkahira, wanda jami’an tsaro suka gano suka kuma kwance shi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.