Zaman takewa :: wane abubuwa akeso mata Susa Dan gyran jiki da xaisa fatarsu tayi kyau da laushi da santsi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Zaman takewa :: wane abubuwa akeso mata Susa Dan gyran jiki da xaisa fatarsu tayi kyau da laushi da santsi

<
Da farko dai kafin ki fara kwalliya akwai bukatar NATSUWA sannan akwai bukatar LOKACI ina nufin wadataccen lokacin da zai isa a awaitar da kwalliya daki-daki kuma a tsare don tabbatar da cewar an yi kwalliyar a natse ba wai kawai a yi ta gara babu ba. Don haka ki tabbatar duk abun da zai dauke maki hankali kin gama da shi.
Abu na biyu kuma shine ki san yanayin fatarki tun daga launinta zuwa gautsi, tauri ko laushinta. Wannan zai ba ki damar sanin ababen kwalliya da za ki harhada wadanda fstarki za ta karba. Saboda sau tari za ka ga wasu sun yi kwalliya amma sam kwalliyar ba ta zauna akan fatarsu ba. Ga yadda za ki gane yanayin fatarki:
YADDA ZA KI GANE YANAYIN FATARKI
Fata mai maiko (OILY SKIN): ko da yaushe za ki ga fatar jikinki tana da maiko ko kin shafa mai ko kirim ko ba ki shafa ba. Kuma da kin goge zuwa wani lokaci za ki ga fatar na nason maiko sannan kuma da kin yi kwalliya za ta narke ta lalace ki yi ta kyalli fauu.
YADDA ZA KI KULA DA FATA MAI MAIKO (OILY SKIN)
Rika yawan yin FACIAL MASK da kwai: Yadda ake yin facial mask na kwai. Za ki fasa kwanki danye, sai ki cire kwanduwar ki bar farin, sai ki rufe fuskarki da tishu fefa (tissue paper), sai ki yi amfani da blusher (wani burushi na shafa kayan kwalliya) ki na dangwalar ruwan kwan kina shafawa a tishu fefar da ki ka lullube fuskarki da ita har sai kowane bangare na fuskar ta ki ta jike da ruwan farin kwan. Za ki bar shi na tsawon mintuna 10 zuwa 15 sai ki wanke da ruwan dumi.
2. Hanya ta biyu na magance maikon fuska ita ce yawan goge fuskarki da lemon zaki ko lemun tsami kafin shafa kayan kwalliya. Yana da kyau ki san cewa yin amfani da nikakkiyar farar shinkafa ki jika ta cikin madara kana ki cuda kafatanin jikinki da ita akalla mintina 20 kafin ki shiga wanka ba wai kawai magance maikon fuska ya ke ba, a’a, hadin na sanya laushi da shekin fata. A kula in ki ka yi wannan hadin ba kya bukatar wanka da sabulu, sai dai akwai bukatar ki yi amfani da ko dai ruwan sanyi ko na dumi wajen dirje jikinki da kyau ta yadda kwabin zai wanku sosai.
3. Hanya ta uku na magance maikon fuska ko fata gaba daya ita ce ki kasance duk man shafawa ko kirim din da za ki saya ya zama an rubuta FOR OILY SKIN (Domin masu maikon fata) ko kuma FOR ALL SKIN TYPES (Domin kowace irin fata) ba wai kawai kamshinsa ya maki dadi ba ko kuma dan shi ake yayi ba ko dan wance ta siya ko yana da tsada ba
A darasi na gaba za mu yi magana akan wani nau’in fata da yadda ake kula da shi kafin daga bisani mu yi bayani akan yadda ake daura musu kwalliya.
Sai dai zan dan yi karin bayani kan yadda za ki wanke fuskarki tare da cire tishu fefar da ki ka lullube fuskarki da ita a yayin da ki ka yi facial mask (kamar yadda na yi bayani a mataki na farko na magance maikon fuska). Ga yadda ake yi: Za ki wanke fuskar da ke lullube cikin tishu faifa da ruwan kwai ne da ruwan sanyi. Sa’annan wankan da za ki yi a lokacin ya zama da zallar sabulu babu soso kuma ya zama da ruwa mai zafi sosai. Sai a wanka na biyu ne wanda watakila da yamma ko da rana za ki yi shi, sai ki yi da soso da sabulu kuma da irin ruwan da ki ke da bukata, ko dai na sanyi ko kuma na dumi.
Wata hanyar har ila yau, ita ce ta hanyar nika bawon lemon zaki ya niku lukwui. sai ki kwaba garin da madara kwabi mai dan kauri. sai ki shafe hadin a fuskarki ki bar shi har na tsawon mintuna 10-15 kafin ki wanke da ruwan sanyi. Wannan ita ma wata hanya ce ta magance maikon fatar fuska.
A darasinmu na yau kuma za mu yi duba ne akan yadda za ki magance matasalar bushewar fata domin ita ma busasshiyar fata tana bada matsala ga nagartacciyar kwalliya.
BUSASSHIYAR FATA: Za ki iya gane busasshiyar fata ce da ke da wadannan alamun: Saurin bushewar fata a lokacin iska ko dari, yawan yi saba, kyasfi, fashewan lebe a lokacin iska ko dari, yawan jin kaikayi da kasancewar fata ta yi fururu kamar an bada miki garin fulawa, yamutsewar fata da sauransu. Ko shakka babu irin wannan fatar ta fi kowace iriyar fata bukatar gyara, kuma wannan darasi ya zo mi ki da hanyoyin magance matsalar bushewar fata.
Hanyoyin Magance Matsalar Bushewar Fata
 • ki daina wanka da ruwa mai zafi domin yana taimaka wa wajen tatse maikon da ya saura gareki
 • ki daina zama a cikin rana mai zafi
 •  kayan sawarki ya kasance mai laushi ba mai gautsi ba
 • ki daina yawan barin jikinki ko wani bangare na jikinki a bayyane musammam a lokacin iska
 • Lebenki ya kasance a kodayaushe ya kasance cikin mai ko basilin ko lip gloss mara kala. Ki kiyayi jambaki na wani dan lokaci ko kuma daga kin gama abun da za ki yi da Jambakin ki goge ki sa lip gloss dinki
 • idan za ki yi burushi da safe ki wanke har da labbanki domin za su yi laushi kuma mataccen fatar leben zai fita. Sai dai ba a goga burushin da karfin tsiya
 • ki dinga yawan shafa madarar yoghurt a fuskar ki ko madara idan ta bushe, sai ki dauraye da ruwan sanyi sosai
 • kada ki rika yawan durje fuskarki kuma kada ki yawaita amfani da Sabulu da yawa
 • ki rika yawan amafani da mayuka da aka yi su da dan itaciyyar APRICOT  ko kuma ya kasance da akwai shi a ciki musamman ma ga kanki
 • ki sayi OATS ki nika shi ya yi laushi sosai idan za ki yi wanka sai ki dibi chokali daya ki zuba a kofi daya na ruwan zafi ki juya idan ya narke sosai sai ki zuba a ruwan wankanki juya da kyau (ruwan wankanki ya zama shi ba mai sanyi ba kuma ba mai dumi ba.
 • Idan kin gama kada ki goge jikinki ki bari fatarki ta shanye ruwan jikin naki.
 • Avocado (piya) ki cire bawon ki yar sai ki dama ta yi laushi ki shafeta a fuskar (kina lailaya fuskarki a hankali) idan ya bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi sosai
 • ki raba ruwan wankan ki biyu, idan kin gama wanka da daya sai ki shafa basilin (vaseline) ko man kade sannan ki watsa sauran ruwan a jikinki. Za ki sake shafa mai in kin fito
 • ki yawaita shafa wa fuskar ki da hannu da kafarki mai duk bayan kowace salla domin sun fi komai bushewa a jikinki
 • idan za ki shafa mai a fuskarki, bayan kin lakato man a hannunki kin mutsuttsika sai ki fara tafa hannunki duk biyun akan fuskar ki a hankali ko ta ina har sai man ya shafu a haka
Kwalliya A Lokacin Zafi
Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.
Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:
•Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.
•Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.
•Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.
•A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.
•Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.
Yadda Ake Kwalliyar Fuska
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska. Ba shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyanr za a iya yin ta a gida idan akwai kayan aiki.
Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ta bushe kafin a shafa mata komai.
•Ana so a samu ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga.
•Bayan an yi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula).
•A samu hodar fandesho dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.
•A samu hoda haka a sake shafawa.
•Sannan sai a samu reza ga wanda ke da cikan gira sai a aske shi kadan.
•A samu gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana girar da shi.
•Bayan haka sai a samu ‘concealer’ da na ‘eye shadow’ da burushin ‘eco tools’ da burushin ‘eyeliner’.
•Sai a fara taje giran da burushin ‘eyeliner’
•Sannan sai a zana girar da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hada su.
•Bayan an shafa sai a sake taje su da ‘eyeliner brush’ din.
•Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a girar.
•A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.
•A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum.
•Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za a saka.
•Sai a shafa jan baki.
Hanyoyin Kulawa Da Fuskarki
Wanke fuska kafin ki kwanta bacci a kowane dare:
 
Me ya sa ya kamata a rika wanke fuska kafin a kwanta barci?
 
Na san kowa zai so ya ji amsar wannan tambaya. Wanke fuska na da matukar muhimmanci ga mace da namiji. Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba. Don haka ya kamata ki canza, ki rika wanke fuskarki kafin ki kwanta barci saboda:
 • Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali da samun barci mai dadi.
 • Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa su fitar da manyan kuraje, inda sai an yi da gaske kafin a rabu da su.
 • Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran fatar jiki.
 • Kada a manta a rika goge fuska da sinadarin ‘cleanser’ kafin a kwanta barci.
 • Ki yi amfani da ‘cleanser’ da ta dace da fatarki kafin a fara amfani da ita wajen wanke fuska.
 • Rashin wanke fuska kafin a kwanta na rage wa mace kyau, domin idan kurajen suka feso a fuska kan samu matsala ko ta canza.
 • Rashin yawan wanke fuska na janyo maruru a fuska.
 • Rashin wanke fuska ko wanka na janyo fitowar kyasbi a fuska, don haka sai a kiyaye.
Yadda Ake Amfani Da Madara Wajen Magance Maikon Fuska
Shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta yi taushi da kuma santsi. Hakan ya sa a yau Mujallar Alummata ta kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance yawan maikon fuska.
Abubuwan bukata
 • Madara
 • Gishiri
 • Ruwa
 • Auduga
 • Zuma
Amfanin madara wajen magance maikon fuska
1. Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
2. Madara na sanya fata santsi: don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
3. Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi: musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
4. Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.
 

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.