Labaran siyasa :: ta faru ta kare mai yasa atiku abubakar yaje kasa amurika - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: ta faru ta kare mai yasa atiku abubakar yaje kasa amurika

<
Karshen dai tika-tika-tik. Bayan cece- kucen da aka rinka yi a Najeriya akan cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Abubakar ba zai iya shiga Amurka ba, a karshe dai ya shiga.
'Yan Najeriya musamman dai 'yan jam'iyya mai mulki ta APC sun ta kalubalantar shi a kan cewa idan ba tsoro ba yaje kasar Amurka.
Atiku Abubakar dai tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya kuma a yanzu haka dan takarar shugabancin kasar ne a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP.
Buhari da Atiku: Amurka da EU na son a rungumi zaman lafiya
Najeriya ta bai wa Amurka shawara kan Atiku Abubakar
Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari
Sau da dama ana ta rade-radin cewa idan Atiku yaje Amurka zai fuskanci dauri sakamakon wani laifi da ya tafka a kasar.
Ya sha dai musanta wannan zargin a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.
Tirkashi, ana wata ga, ga wata. Mulki ta bar arewa ta yamma ta koma arewa ta gabas. Allah ya nuna mana mulkin @atiku .
— Atikulated2019 (@Utchay_dbold) 17 Janairu, 2019
Malam @BashirAhmaad a gaya wa baba @MBuhari da magoya bayanshi fa. Shugaba mai jiran gado
@atiku ya isa DC, saura #AsoRock Bijahi Nabiyul Ummi (SAW)
— khalifa (@usmanwaziri2) 17 Janairu, 2019
Wannan photoshop/hade-hade ne ni ban yarda yaje ba in kuma yaje to yakamata mu ganshi tare da wani babban baamurke
— Dahiru Ahmad Ali (@DahiruAhmadAli1) 18 Janairu, 2019

Sai dai a ranar Alhamis 17 ga watan Junairu ne kwatsam aka ga hotunan Atiku suna yawo a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa ya je Amurka.
An dai ga tsohon mataimakin shugaban kasar ne tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a cikin hotunan.
Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, yana ziyara a Amurka ne domin ganawa da manyan jami'an gwamnati da 'yan kasuwan kasar da kuma 'yan Najeriya mazauna Amurka.
Sai dai a wata hira da Atiku ya yi da BBC a kwanakin baya, ya bayyana cewa ya nemi izinin shiga Amurka, amma an hana shi.
Ko da aka tambaye shi a kan batun gidansa na Amurka da aka yi gwanjonsa sai ya bayyana cewa gidan matarsa ne da ya saya mata a kasar kuma ita ta sayar da gidan nata.
A hirar dai ya bayyana cewa ba dole ba ne sai mutum ya je Amurka kafin ya zama shugaban kasar Najeriya, babu inda aka fadi haka a kundin tsarin mulki, in ji Atiku.
Tun bayan isar Atiku Amurka, tuni dai mutane da dama suke sharhi suna tafka muhawara a shafukan sada zumunta akan wannan batu.
Da dama wasu daga cikin magoya bayansa a shafukan sada zumunta suna ta murna a kan cewa gwaninsu ya shiga Amurka, wasu kuma har yanzu ba su yarda ba inda suke ganin cewa kamar hada hotunan aka yi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.