Labaran siyasa ::: Shugaban PDP a cikin Jihar Kebbi ya sauya-sheka zuwa APC - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Shugaban PDP a cikin Jihar Kebbi ya sauya-sheka zuwa APC

<
Shugaban jam’iyyar PDP mai adawa na karamar hukumar Augie a jihar Kebbi ya sauya-sheka. Daily Trust ta rahoto cewa Mohammed Musa Bayawa Augie ya fice daga PDP ne ya koma jam’iyyar APC.
Jam’iyyar PDP ta sake yin wani babban rashi a Jihar Kebbi
Alhaji Musa Bayawa Augie wanda yake shugabantar jam’iyyar adawa ta PDP a garin na Augie ya rungumi APC ne yayin da kusan wata guda ya rage a soma zabe a Najeriya. Augie yace PDP ba ta tsinana masu komai ba tun 1999.
Haka kuma akwai wasu dinbin ‘yan PDP a jihar da su ka koma APC a jihar. Sama da mutane 150 daga jam’iyyar PDP a karamar hukumar Maiyama su ka koma jam’iyyar APC a jihar Kebbi. APC tayi alkawarin tafiya da kowa a jihar.
KU KARANTA: Tun wuri APC ta shirya shan kashi a hannun Atiku- PDP
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Sani Bala Kangiwa, shi ne ya karbi sabbabin shiga jam’iyyar a garin Birnin Kebbi. Tsofaffin ‘ya ‘yan na PDP sun yi alkawarin yi wa APC yaki tukuru a zaben da za ayi kwanan nan.
Kwanan nan ne dai Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kebbi gaba daya watau Muhammadu Sakaba, ya fice daga jam’iyyar adawar ya koma APC. A kwanakin baya kuma PDP ta rasa Buhari Bala da wasu kusoshi zuwa APC.
Idan ba ku manta ba, kwanaki kun ju cewa Uwargidar gwamnan jihar Kebbi, Dr. Zainab Bagudu ta fara bi gida-gida domin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen don ganin ya zarce a zaben 2019

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.