Labaran siyasa ::: Saura kwana 28 zaben 2019: Bayani kan 'yar takara Obiageli Ezekwesili - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Saura kwana 28 zaben 2019: Bayani kan 'yar takara Obiageli Ezekwesili

<
Obiageli Ezekwesili tsohuwar mataimakiyar shugaban Bankin Duniya ce, sannan kuma ta rike mukaman ministan ilimi da kuma ma'adanai a Najeriya.
Sabanin sauran manyan 'yan takara, Mis Ezekwesili kirista ce wadda ta fito daga yankin kudancin Najeriya, kuma jam'iyyar da take yin takara a karkashinta karama ce idan aka kwatanta da tasu.
Ta jagoranci kamfe na Bring Back Our Girls wanda ya ja hankalin duniya baki daya bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai 300 daga garin Chibok na jihar Borno da ke Arewa maso gabshin Najeriya.
Oby Ezekwesili ta shirya karawa da Buhari a zaben 2019
'Ya kamata a yi bayani kan asusun Nigeria'
Masana na ganin cewa kwarewarta kan tattalin arziki baiwa ce ga Najeriya sai dai rashin goyon baya daga manyan 'yan siyar kasar ka iya kawo mata tsaiko.
Ta yi alkawarin cewa in dai aka zabe ta za ta sauya fuskar tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da man fetur da kuma samar wa matasa aikin yi.
"Yar shekara 55, Mis Ezekwesil tana hankoron zama shugabar kasa mace ta farko a Najeriya duk da cewa abu ne mawuyaci a kasar da maza suka yi kaka-gida.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.