Labaran siyasa :: sako zuwa ga magoya bayana inji atiku abubakar - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: sako zuwa ga magoya bayana inji atiku abubakar

<
Atiku yace kowa ya kare kuri'arsa
- Yayi alkawarin sabbin tsare tsare a bangaren tatalin arziki
- Yace zai tabbatar da tsaro
Ku jefa quri'a, ku raka, ku tsare, ku jira a qirga, Atiku ya kira 'yan Najeriya
Dan takarar shugabancin kasar nan a babban jamiyar adawa PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar zai kawo sabbin canja canjee idan har yayi nasarar zama shugabancin kasar Nigeria a zabe me zuwa.
Ya kuma yi kira ga masu kada masa kuri'u da kada su bar wurin zabe, domin kada a murde musu, in sunn jefa su tsaya su raka su jira a kirga.
Ya bayyana hakan ne a ranar talatar da ta gabata lokacin da garin Owerri a lokacin da yakai ziyarara yakin neman zabe a kudu maso gabashin kasar nan.
Ku jefa quri'a, ku raka, ku tsare, ku jira a qirga, Atiku ya kira 'yan Najeriya
Ya dai tabbatar da cewa zai kawo canji a bangaren tattalin arziki Wanda zai karawa wa harkar kasuwanci daraja da kuma fadada harkar ga inyamuran kasar nan.
Sannan yace zai tabbatar da cikakken tsaro ga dukkan bangaren batare da nuna bambancin kabila ko addini ba.
GA WANNAN : Wadansu tsirarun 'yan Najeriya a kasashen waje na can suna taya Atiku murnar isowa kasashensu, da kushe
Ofishin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewar yakin neman zaben wanda aka gudanar a filin wasa na Dan Anyim yayi cikar Kwari, sauran abubuwan da suka gudana a gurin sun hada sa bada tuta ga dan takarkarun gwamnonin a jam'iyar ta PDP na kudu maso gabashin.
Cikin mutanen da suka halarci taron sun hada da Mr Peter Obi mataimakin dan takarar shugabancin kasar, da kuma kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki da kuma shugabancin jamiyar PDP ta kasa Mr uche Sekondus da dai sauran jiga jigan yan jam'iyar adawar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.