Labaran siyasa :: Maine dalilin su Ban da mu a mubaya'ar da Makiyaya su kayi wa Buhari - Kungiyar Gan Allah - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Maine dalilin su Ban da mu a mubaya'ar da Makiyaya su kayi wa Buhari - Kungiyar Gan Allah

<
Kungiyar nan ta “Gan Allah Fulani Development Association” ta Najeriya ta bayyana cewa ba ta cikin wadanda su kayi wa shugaba Muhammadu Buhari mubaya’a kamar yadda ake ta yadawa Duniya.
Ban da mu a mubaya'ar da Makiyaya su kayi wa Buhari - Kungiyar Gan Allah
Wasu Fulani sun ce ba su yi wa Shugaban kasa Buhari mubaya’a ba
Sakataren wannan kungiyar Fulani ta Gan Allah, Ibrahim Abdullahi, yayi watsi da goyon bayan da wasu ‘Yan uwan su su ka ba gwamnati mai-ci ta shugaba Buhari. Abdullahi yace kungiyar su, sam ba ta goyon bayan wannan mataki.
Ibrahim Abdullahi yace ba za su bari wannan mataki da wasu tsirarrru su ka dauka ya tsaya ba, a cewar sa, lamincewa hakan yana iya kawo gaba tsakanin Fulani da ke Najeriya. Abdullahi ya bayyana wannan ne a Ranar Larabar nan.
Kungiyar ta Gan Allah ta bayyana cewa marawa Buhari baya a 2019, zai jefa mutanen kasar cikin karin wahalar rayuwa, don haka ne kungiyar tace babu ruwan ta da wadanda su ka ari bakin su, su ka nuna goyon baya ga Shugaba Buhari.
KU KARANTA: Makiyayan Najeriya za su marawa Buhari baya a zaben 2019akataren wannan kungiya yace matakin da Takwarorin na su su ka dauka, bai dace ba, domin kuwa an nuna tsantsar son rai. Kungiyar tace wadanda su kayi wa Buhari mubaya’a, su na kokarin gyara miyar su ne, ko da kowa zai rasa.
Kungiyar ta Gan Allah, tace za ta rika yawo ruga bayan ruga domin wayar da kan ‘yan uwan su a zaben 2019. Ibrahim Abdullahi, yayi kaca-kaca da yadda sauran kungiyoyin Fulani su ka tsunbula cikin sha’anin siyasa tsamo-tsamo a kasar.
Kwanaki kun ji cewa Makiyayan Kasar nan a karkashin Kungiyar ‘Yan Miyetti Allah sun tsaida Muhammadu Buhari na APC a matsayin ‘Dan takarar su na kujerar Shugaban kasa a zabe mai zuwa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.