Labaran siyasa ::: mai yasa Atiku ya fadi haka Idan har ana son kawo karshen Boko Haram, sai an sauke Buhari a 2019 - Atiku - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: mai yasa Atiku ya fadi haka Idan har ana son kawo karshen Boko Haram, sai an sauke Buhari a 2019 - Atiku

<
Atiku Abubakar, ya yi ikirarin cewa kashe kashen da Boko Haram ke yi zai ci gaba da munana, ma damar aka sake zabar Buhari a karo na biyu
- Atiku ya zargi Buhari da bata lokaci, kudade da kayan aiki wajen yakin zabe, yayin da Boko Haram da ke ci gaba da salwantar da rayukan 'yan Nigeria
- Ya bukaci Buhari da ya gaggauta soma bincike kan zargin cin hanci da rashawa, na salwantar biliyoyin daloli, wajen sayen kayan yaki ga dakarun soji
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi ikirarin cewa kashe kashen da Boko Haram ke yi zai ci gaba da munana, ma damar 'yan Nigeria suka sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.
Atiku a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren ranar Litinin, ta hannun babban mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Phrank Shaibu, ya zargi gwamnatin tarayya da bata lokaci, kudade da kayan aiki wajen yakin zaben Buhari, yayin da suka yi kunnen uwar shegu da ta'addancin Boko Haram da ke salwantar da rayukan 'yan Nigeria.
Da yake martani kan harin da Boko Haram ta kai a wasu sansanonin soji biyu a jihar Borno a ranar Alhamis, Atiku ya ce idan da ace Buhari ya batar da rabin kudi da lokacin da bata wajen yakin zabensa akan ta'addancin Boko Haram, da hakan magance matsaloli da dama, tare da kare rayuka da dama daga salwanta.
Idan har ana son kawo karshen Boko Haram, sai an sauke Buhari a 2019 - Atiku
Idan har ana son kawo karshen Boko Haram, sai an sauke Buhari a 2019 - Atiku
Ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya gaggauta soma bincike kan zargin cin hanci da rashawa, da yayi salwantar biliyoyin daloli, wajen sayen kayan yaki ga dakarun soji, da ya hada da kayan abincinsu, wanda kuma tuni rahotanni suka bayyana na cewar ba a sayi komai da kudin da aka ware ba.
Dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, ya yi ikirarin cewa, "Buhari ba zai iya magance cin hanci da rashawa da aka tafka a wajen sayen kayayyakin sojin ba, duk da cewa akwai rahoton hakan da kamitin binciken badakalar ya gabatar masa tun daga 2007 har zua 2015
"Buhari da masu bashi shawara kan harkokin tsaron kasar na sane da kwafin wannan rahoto, kuma tabbas zasu iya shiga cikin jama'a da zaran anso hakan, amma aka dakile kwamitin don kar 'yan Nigeria su san irin cin hancin da aka tafka, wanda har yanzu ana kan tafkawa."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.