Labaran siyasa ::: Kuri’un Buhari bana sai sun zarce abin da ya samu a 2015 – Gwamnan Kebbi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Kuri’un Buhari bana sai sun zarce abin da ya samu a 2015 – Gwamnan Kebbi

<
Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu yayi alkawarin ganin cewa jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaben da za ayi kwanan nan. Saura dai makonni 4 yanzu rak a gudanar da zabe a kasar.
Atiku Bagudu yace Buhari zai samu makukun kuri'a a jihar sa
Mai Girma Atiku Bagudu ya sha alwashin ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da tarin kuri’un da ba a taba samun su ba a fadin jihar. Bagudu yace abin da Buhari zai samu a zaben bana sai ya haura kuri’un sa na zaben 2015.
Sanata Atiku Bagudu na jam’iyyar APC yayi wannan jawabi ne a wajen wani kamfe da Mai dakin sa watau Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta shiryawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin garin Birnin Kebbi a tsakiyar makon nan.
KU KARANTA: Kan Malaman addini ya rabu a game da zaben Buhari da Atiku
Gwamnan ya fadawa dubban jama’an da su ka halarci wannan taro na yakin neman zabe cewa Buhari zai tashi da kuri’un da bai taba samun su ba tun da yake takara a jihar. Buhari yana neman zarcewa ne wannan karo a kan mulki.
Gwamna Atiku Bagudu dai ya yabawa irin gayyar da Matar sa Zainab Shinkafi Bagudu ta tara a jihar. Gwamnan yace dandazon jama’an da su ka fito wajen kamfen din ya nuna yadda matasa da mata ke tare da shugaban kasa Buhari.
Idan ba ku manta ba, a zaben 2015 da aka yi, shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’u sama da 560, 000 ne yayin da jam’iyyar da ke mulki a lokacin watau PDP ta tashi da kuri’u kusan 100,000 rak.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.