Labaran siyasa ,::: Kaiwa Buhari farmaki kai tsaye: PDP ta fara wuce gona da iri - Garba Shehu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ,::: Kaiwa Buhari farmaki kai tsaye: PDP ta fara wuce gona da iri - Garba Shehu

<
Fadar shugaban kasa ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP na yin kan mai uwa da wabi a yunkurin da take yi na cimma muradun kashin kanta na siyasa
- Ta ce PDP ta dauki wani shiri na gudanar da wasu ayyuka da ka iya kawo tarnaki a dorewar tsarin demokaradiyyar Nigeria
- Hakika lokaci yayi da 'yan Nigeria zasu rabe tsakanin aya da tsakuwa kuma su gane cewa babu abunda suke yi illa bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari
A ranar Talata, fadar shugaban kasa ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP na yin kan mai uwa da wabi a yunkurin da take yi na cimma muradun kashin kanta na siyasa.
Garba Shehu, babban mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar watsa labarai, ya ce PDP ta dauki wani shiri na gudanar da wasu ayyuka da ka iya kawo tarnaki a dorewar tsarin demokaradiyyar Nigeria.
Ya yi Allah-wadai da irin hare haren zafafan kalamai da jam'iyyar adawar ke yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin jam'iyyar APC.
KARANTA WANNAN: Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB
Kaiwa Buhari farmaki kai tsaye: PDP ta fara wuce gona da iri - Garba Shehu
Shehu a cikin nata sanarwa ya ce: "Mun karanta sanarwa da dama da jam'iyyar PDP ta rabawa manema labarai, inda suke kan bakansu na kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari farmaki.
"Hakika wannan abun Allah-wadai ne, musamman ma ace batancin na fitowa daga jam'iyyar da ta wuce gona da iri a lalata demokaradiyya. Yin batanci ga gwamnati ko rashin kunya ga na-gaba, ba zai zama adawa ta siyasa ba.
"Ganin yadda jama'a ke bin tafarkin PDP da shuwagabanninsu abun takaici ne amma abun takaicin shine yadda PDP ke son yin kan mai uwa da wabi a dukkanin lamuranta na son rai da burin ganin su sake samun mulkin kasar.
"Duk da hakan, kullum suna ci gaba da rasa mambobinsu a dango-dango, kuma sam babu wani armashi na yakin zabensu. Hakika lokaci yayi da 'yan Nigeria zasu rabe tsakanin aya da tsakuwa kuma su gane cewa babu abunda suke yi illa bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.