Labaran siyasa :: Irin halayen Abacha gare ka, Obasanjo ya sake rubuta buddadiya ga Buhari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Irin halayen Abacha gare ka, Obasanjo ya sake rubuta buddadiya ga Buhari

<
A yau, Lahadi, ne tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasajo, ya sake raba wata budaddiyar wasika da ya rubuta zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ga manema labarai, in da ya caccaki shugaban kasar tare da zarginsa da yunkurin yin magudi a zabukan da za a yi cikin watan Fabrairu.
Shugaba Buhari ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki a zaben 'yan takarar shugaban kasa da mambobin majalisar tarayya da za a yi ranar 16 ga watan Fabrairu.
A cikin budaddiyar da Obasanjo ya raba ga 'yan jaridu yayin wani taron manema labarai da ya kira a dakin sa na karatu da ke Abeokuta, jihar Ogun, Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da nuna halayya irin ta tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Marigayi Janar Sani Abacha.
" Buhari ya yi nasarar yaudarar mu a karo na farko, zamu zama wawaye idan mu ka bari ya sake yaudarar mu a karo na biyu," a cewar Obasanjo.
Sannan ya cigaba da cewa " Buba Galadima, tsohon sakataren jam'iyyar CPC da Buhari ya kafa, ya fito ya gargadi jama'a cewa duk alkawarin da Buhari zai dauka, ba zai taba canja halinsa ba. Galadima ya san Buhari sosai kuma sun dade suna gwagwarmayar siyasa tare ."
Obasanjo da Buhari
A cikin wasikar ta sa, Obasanjo ya ce Galadima ya bayyana shugaba Buhari a matsayin " mutum mai ra'ayin rikau, maketaci, maras hakuri, da ba ya taba karbar laifinsa a lokutan da al'amura su ka tafi ba daidai ba kuma ba ya daukan shawara. Duk wanda ba zai iya gyara zuciyar sa ba, ba zai iya gyara komai ba, kamar yadda Bernand Shaw ya taba fada ."
Obasanjo ya kara da cewar za a iya abubuwan da ke faruwa a Najeriya a yanzu da irin yadda abubuwa su ka faru lokacin mulkin soja na Abacha.
" Shine ya ke bawa Abacha shawarar ya azabatar da mutane ko ya kashe su a wancan lokacin, yanzu ma kuma irin wannan turbar ya ke sake son komawa ," a cewar Obasanjo.
DUBA WANNAN: Tuhumar Onnoghen: Ana yiwa rayuwa ta barazana - Tsohon hadimin Buhari
Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa, tuni shugaba Buhari da jam'iyyar APC sun dauki hayar ma'aikatan zabe da zasu sanar da sakamako na bogi da aka rubuta aka ba su.
Obasanjo ya yi zargin cewar Buhari da APC na shirin yin amfani da tashin hankali lokacin zabe domin ganin sun samu damar cimma manufar su ta yin magudi.
Budaddiyar wasikar ta Obasanjo na zuwa ne a lokacin da shugaba Buhari ya jaddada cewar zai tabbatar an yi zabe na gaskiya da kowa zai gamsu da sakamakon sa.
Ya zuwa yanzu dai fadar shugaban kasa ba ta mayar da martani ko yin raddi ga Obasanjo ba a kan wannan zarge-zargen da ya yiwa Buhari a cikin budaddiyar wasikar da ya rubuta ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.