Labaran siyasa :: Dalilin da yasa nake neman Karin shekaru 4 akan mulki – Buhari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Dalilin da yasa nake neman Karin shekaru 4 akan mulki – Buhari

<
Shugaban Buhari yace yana neman tazarce a zaben 2019 domin ya karfafa nasarorin da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa, rashin tsaro da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki
- Yace jam’iyyar APC ta zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa saboda ya cika alkawaran zaben da ya dauka na jam’iyyar
- Kan zargin cewa akwai bangarenci a yaki da rashawa, Buhari yace zargin ba gaskiya bane
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace yana neman tazarce a zaben 2019 domin ya karfafa nasarorin da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa, rashin tsaro da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki.
Mista Buhari ya bayyana hakan ne a wani taro da gidauniyar MacArthur tare da kafofin watsa labarai na NTA da DARIA suka shirya a Abuja a ranar Laraba, 16 ga watan Janairu.
Yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa saboda ya cika alkawaran zaben da ya dauka na jam’iyyar.
Dalilin da yasa nake neman Karin shekaru 4 akan mulki – Buhari
Kan zargin cewa akwai bangarenci a yaki da rashawa, Buhari yace zargin ba gaskiya bane.
A cewarsa, babu wani da aka zarga da rashawa tare da hujja sannan suka dauke idanunsu.
Shugaan kasar yace yana taka-tsan-tsan saboda ba za a iya kama mutane cikin sauki ba a gwamnatin damokradiyya sannan a kai su kotu ba tare da kwakwarar shaida ba.
KU KARANTA KUMA: Kwamishinonin yan sanda da sauransu sun je Abuja, suna neman kamun kafa da sabon IGP
Ya yi kira ga yan Najeriya da su tallafa wa gwamnati sannan su tona mutane, kungiyoyi da kamfanoni masu aikata rashawa.
A cewarsa za a mika wadannan mutane ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sannan cewa sun aminta da tsarin da za a bi akan lamarin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.