Labaran siyasa ::: Buhari zai kauracewa Kano saboda Ganduje - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Buhari zai kauracewa Kano saboda Ganduje

<
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna shakku a kan ziyartar jiha Kano domin yakin neman zabe saboda rashin amsar da zai bawa Kanawa idan sun tambaye shi a kan faifan bidiyon zargin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da karbar cin hanci.
Majiyar mu ta ce batun faifan bidiyon gwamna Ganduje na karbar cin hanci daga hannun wasu da ake zargin 'yan kwangila ne ya kara tasowa a wurin taron kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, lamarin da ya sa Buhari nuna kokonto a kan zuwa Kano kamfen.
A cikin shekarar da muka yi bankwana da ita ne wasu faifan bidiyo dake nuna gwamna Ganduje na karbar kudi da ake zargin cin hanci ne suka bayyana a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta.
Buhari da Ganduje
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar ba lallai Buhari ya ziyarci Kano ba saboda badakalar da ake zargin Ganduje da ita.
An yi taron kwamitin ne domin tattauna hanyoyi da dabarun yakin kamfen din shugaba Buhari.
DUBA WANNAN: EFCC ta kama wani mutum da N75m a filin jirgin sama na Kano, hoto
Mamba a Kwamitin, Bashir Lado, ya nuna damuwarsa a kan jadawalin yakin neman zaben, yana mai bayar da shawarar cewar a saka jihohin Kano da Lagos a karshe saboda yawan jama'ar da suke da shi.
Da yake mayar da martani a kan kalaman Lado, Buhari ya tambaye shi " wacce amsa zan bawa mutanen Kano idan suka tambaye ni me yasa gwamnansu ke murmushi yayin karbar cin hanci?"
"Bani da amsar da zan basu. Ba zan iya zuwa Kano kamfen ba idan ba tilas hakan ya zama ba," Buhari ya fada ga yayin ganawar sirri da mambobin kwamitin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.