Labaran siyasa ::: Barayi sun shiga ofisoshin Sanatoci 3, sun saci abubuwa masu tsada - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Barayi sun shiga ofisoshin Sanatoci 3, sun saci abubuwa masu tsada

<
Wasu bata gari da ake kyautata zaton barayi ne sun balle kofofin ofisoshin wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya ukku inda suka shiga suka saci wasu muhimman abubuwa masu tsada, kamar dai yadda muka samu labari daga majiyar mu ta Nishadi Tv.
Barayin dai sun washe ofishin Sanata mai wakiltar Lagos ta yamma, Sanata Remi Tinubu inda suka kawshe kwamfitoci da wasu kayayyakin ofis.
Da dumin sa: Barayi sun shiga ofisoshin Sanatoci 3, sun saci abubuwa masu tsada
KU KARANTA: Jiga-jigan APC sun koma APC a Jigawa
Sai kuma ofishin Dan majalisar wakilai mai wakiltar Ringim/Taura a zauren majalisar wakilai, Muhammad Gausu Bayi inda suka sace talabijin da wayoyi da sauran kayayyakin amfani.
Haka kuma barayin sun shiga ofishin Dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara, Mu'azu Lawal inda suka balla ofishin suka washe shi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.