Labaran siyasa ::: Ana wata ga wata anshiga takun saka Tsakani Aisha Buhari da wani gwamna imo - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa ::: Ana wata ga wata anshiga takun saka Tsakani Aisha Buhari da wani gwamna imo

<
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, hargitsi ya auku tsakanin magoya bayan 'yan takarar gwamna na jam'iyyar APC da AA a jiya Asabar cikin filin wasanni na Dan Anyiam da ke birnin Owerri na jihar Imo.
Mun samu cewa an yi hargitsi tsakanin magoya bayan dan takarar gwamnan jihar Imo na jam'iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma, da kuma na jam'iyyar Action Alliance (AC), Uche Nwosu a jiya Asabar cikin birnin Owerri.
Tsanani irin na adawar siyasa ya kara harzuka sakamakon rashin jituwa da ta auku tsakanin uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari, da kuma gwamnan jihar, Rochas Okorocha, yayin da ya bugi kirjin cewa, dan takarar jam'iyyar AC da ya kasance dan uwa a gare sa shine zai lallasa na jam'iyyar APC a zaben watan jibi.
Aisha Buhari da Rochas sun shiga takun saka kan goyon bayan dan takarar gwamnan jihar Imo
Aisha Buhari wadda Dolapo Osinbajo, uwargidan mataimakin shugaban kasa ta wakilta yayin babban taron, ta yi kira ga dumbin al'ummar jihar da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC a yayin babban zabe na kasa.
Furucin gwamna Rochas ya fusata jagorori da manyan mata na jam'iyyar APC da suka yi tattaki domin halartar taron daga jihohi biyar na yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, da ya sanya suka kama gaban su ba bu shiri.
KARANTA KUMA: Kungiyar hadin gwiwar jam'iyyu ta kalubalanci Buhari kan jagorantar yakin neman zaben sa
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, al'umma sun bai wa idanun su hakki yayin shaidar dan karamin yakin da aka fafata a tsakanin magoya bayan gwamnan jihar Rochas da kuma na dan takara Uzodinma a harabar wasannin ta Dan Anyiam.
Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, wannan hargitsi ya sanya jami'an tsaro suka ribaci makaman su wajen kwantar da tarzoma. Sai dai an yi rashin wasu Mata biyu sun raunata da a halin yanzu su na ci gaba da samun kulawa a gadon asibiti.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.