Labaran Duniya ::: shine .mai yasa polesi suka gaiyachi trump - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya ::: shine .mai yasa polesi suka gaiyachi trump

<
Majalisar wakilan Amurka ta amince da wani kuduri da nufin kawo karshen mako biyu na rufe wasu bangarorin ayyukan gwamnatain kasar, wanda ya samo asali daga rashin jituwa kan bukatar shugaba Donald Trump na gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.
Majalisar ta amince da ci gaba da samar da kudade ga ma'aikatar tsaron cikin gida, har zuwa watan gobe, da kuma na wasu ma'aikatun har zuwa karshen watan Satumba.
Ba su dai samar da kudaden da shugaba Trump ke bukata na gina katangar ba. Ya kuma dage kai da fata cewa ba zai amince da duk wani mataki da suka dauka ba, matukar bai kunshi dala biliyan biyar na gina katangar ba.
An dauki wannan matsaya ne jim kadan bayan jam'iyyar Democrats ta karbi shugabancin majalisar tare da nada Nancy Pelosi a matsayin shugaba.
Nancy Pelosi tsohuwar 'yar siyasa ce kuma, tsayayya da ba ta tsoro, watakil dalilin da ya sanya jim kadan bayan zabar ta a matsayin shugabar majalisar wakilai suka tashi haikan dan samar da kudurin dokar da zai kawo karshen makwanni biyun da aka dauka wasu bangarorin ayyukan gwamnati sun tsaya cak.
Tun a jiya alhamis Pelosi ta rubutawa shugaba Donald Trump wasika wadda a ciki ta bukaci ya gabatar da jawabi ga 'yan majalisa a ranar 16 ga wannan watan, kafin ita kuma ta fara aiki a ranar 29 ga watan.
Bayan aikewa Mr Trump ne ta wallafa wannan wasika a shafinta na twitter, goron gayyatar gabatar da jawabin shekara ga shugban Amirkar na zuwa ne a daidai lokacin da rashin jituwa t yi kamari tsakanin Mr Trump da 'yn mjlisar.
Ta kuma shaidawa manema labarai dole a dauki mataki dan magance matsalar, ta kuma kira gina ktanga tsakanin kasashe biyu da abin da bai da ce ba da barntar da dukiyr kasa sannan tsohon tunani ne na magance kwarrar yan cirani. Mai makon gina katanga gara an karawa jami'an da ke kula da iyakokin kasr walwala dan samun kwarin gwiwar gudnr da yyuknsu

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.