Labaran chikin kasa Nigeria :: yay gareka gobe ga Dan uwanka Allah yasa mudace - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: yay gareka gobe ga Dan uwanka Allah yasa mudace

<
Wasu ‘yan bindiga a kan Babura suka kai hari da yammacin ranar Lahadi a garuruwa uku da suka hada da Warwanna da Kursa da kuma Dutse, duk a gundumar Gandi ta karamar hukumar mulki ta Rabah a jihar Sokoto.
Maharan sun yi harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da yayi sandiyyar mutuwar akalla mutane 26.
Harin ya tarwatsa alummar garuruwan guda uku, to amma daga bisani an samu tattarar jama’a da jami’an tsaro, inda aka je neman gawarwaki, aka kuma samu 26 da aka yi musu jana’iza da yammacin Litinin.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya dage gudanar da taron gangamin yakin neman zabensa da aka tsara gudanarwa a Goronyo dake makwabtaka da karamar hukumar Rabah da lamarin ya auku, inda kuma ya halarci jana’izar mamatan.
Ya jajantawa iyalai da al’ummar yankin akan wannan ibtila’in kuma ya yi alkawarin gwamantinsa zata ci gaba da daukar matakai na tabbatar da cewa an tsare al’umma da dukiyoyinsu. Yace shugabanni da jami’an tsaro na jihar Sakkwato da gwamnati suna iya kokarinsu wurin kawo karshen wannan lamari.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto Murtala Mani, na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar, ya kuma ce jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin. Ya kuma ce suna hadin gwiwa da sojoji da jami’an tsaron farin kaya domin wannan yaki.
Wannan ne karo na biyu da ake kai irin wannan harin a gundumar Gandi. An kai harin na farkon ne a garin Tabanni a ranar tara ga watan Yulin da ya gabata, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka 32.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.